Tsananin cin amanar aure ya sa Kotu ta saki wata Mata cikin watan Azumi a jihar Arewa


Wata Kotu ta Upper Area dake Gwagwalada, Abuja, ta raba auren shekara 15 da aka yi tsakanin wani ma’aikacin gwamnati, Okpanachi Yahaya da matar sa, Zainab Adejoh bisa rashin aminci.

 Alkalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkareem, ya raba auren kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, bayan rokon da Yahaya ya yi na sakin aure bisa dalilin rashin aminci. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

 Alkalin Kotun Abdulkareem ya umarci Zainab Adejoh da ta yi “Iddah” na tsawon wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kafin ta sake yin wani aure.

 Ya kara da cewa batun kula da yara da mai shigar da kara ya gabatar a gaban kotu ya kamata a shigar da shi a matsayin wata kara ta daban.

 Tun da farko dai wanda ya shigar da kara ya shaidawa kotun cewa ya auri wanda ake kara bisa shari’ar Musulunci a ranar 14 ga Satumba, 2019 kuma suna da ‘ya’ya biyu masu shekaru 14 da 12.

 Ya ce ya lura cewa wanda ake kara ta fara cin amanar aure a shekarar 2019.

 "Na ga Zainab tana boye a cikin kicin tana magana da wani mutum kuma da na yi mata tambayoyi, sai ta yi min duka ta zazzageni," in ji Yahaya.

 Ya ce ya yi rashin lafiya na tsawon watanni hudu, an kwantar da shi a asibiti, daga bisani kuma aka kai shi kauyensu da ke Kogi amma wanda ake kara batq taba ziyartar shi ba kuma ta ci gaba da mu’amalar ta na cin amanar aure.

 Ya ce wanda ake kara ta je ofishin sa inda yake aiki a lokacin da yake can kauyen yana jinya, ta karbi kudi a madadinsa ba tare da izininsa ba.

 Yahaya ya ce an gano cewa tushen ciwon nasa ya samo asali ne daga haramtacciyar alaka da wanda ake kara ta ke yi da wasu mazan.

 “’Yan uwana sun gayyace Zainab domin sasanta rikicinmu amma ta ki zuwa.

 "Babu sauran soyayya da zaman lafiya a cikin wannan auren,  Ina son a raba auren," in ji shi.

 Sai dai wanda ake kara ta amince da a raba auren.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN