Da dumi-dumi: An kori Yan sanda 3 daga aiki da suka yi wa Mawaki Rarara rakiya suka yi harbin bindiga


Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sallami jami’anta uku da aka kama suna harbin bindiga don yabon wani mawaki Dauda Kahutu ‘Rarara’ a jihar Kano kwanan nan
.

 A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu, jami’an da ke yi wa mawakin rakiya, sun bude kofa ga wata mota kirar SUV da ya shiga sannan suka yi ta harbe-harbe ta sama suna yi masa rakiya yayin da magoya bayansa suka taru suna taya shi murna.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu, ta ce bayan korafe-korafe da bincike kan hujjojin bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta, jami’an da ke aiki da sashin kariya na musamman (SPU) Base 1 Kano.  

An yi masu shari’a cikin tsari mai kyau na Yan sanda, kuma an kore su daga aiki saboda laifukan rashin da'a da amfani da makami ba bisa kaida ba, cin zarafi, da almubazzaranci da harsashi.

Mutum uku, Inspr.  Dahiru Shuaibu, Sgt.  Abdullahi Badamasi, da Sgt.  Isah Danladi sun kasance tare da wani mawaki a Kano yana aikin rakiya.  

A yayin gudanar da aikinsu a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023 a kauyen Kahutu, jihar Katsina, jami’an sun yi ta harbin bindiga a sama duk da manufofin ‘yan sanda na hana harbe-harbe a iska, tsarin aiki da kuma umarnin rundunar da abin ya shafa;  da kuma yin barazana ga taron jama'a a wurin wanda ya hada da yara.  

Wannan aika aika ba kawai laifi ba ne da rashin da’a amma kuma abin kunya ne ga rundunar da kasa baki daya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN