Yan Fashi Da Makami Sun Kai Mummunan Hari Kasuwar Ogun Da Tsakar Rana, Sun Kashe Wani Dan Kasuwa


Wasu da ake zaton masu fashi da makami ne sun farmaki shahararriyar kasuwar wayoyi da kayan wuta da aka fi sani da 'Computer Village' a Abeokuta, jihar Ogun inda suka kashe wani dan kasuwa. Legit ya wallafa.

Yan bindigar da yawansu ya kai takwas sun farmaki kasuwar da ke Oke-Ilewo, Abeokuta, da tsakar ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu don aiwatar da aika-aikarsu, Daily Trust ta rahoto.

Shaidu sun ce maharan na ta harbe-harbe, lamarin da ya haddasa tashin hankali tsakanin yan kasuwa inda suka tarwatse don neman mafika.

Sai dai kuma, wasu shaidu sun kuma yi zargin cewa yan bindigar na iya kasance mambobin kungiyar asiri da ke bibiyan abokan hamayyarsu ne.

An tattaro cewa wasu matasa masu ciniki a kasuwar sun dakile harin daga bisani inda suka kama mutum daya.

Rundunar yan sanda ta yi martani
Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, cewa yan sandan sun yi nasarar dakile fashin.

Oyeyemi ya fada ma manema labarai cewa:

"Guggun yan fashin sun farmaki kasuwar da misalin karfe 5:30 na yamma, suka fara harbi kan mai uwa da wahabi sannan suka sace tsadaddun wayoyi."

Ya bayyana cewa an yi wani kira mai cike da damuwa ofishin yan sandan Ibara sannan DPO na yankin, CSP Abayomi Adeniji, ya gaggauta tura yan sandan yaki da fashi da makami tare da tawagar hadin gwiwa na Amotekun zuwa wajen.

A cewarsa, da hango yan sandan, yan bindigar sun yi musayar wuta da su amma saboda karfin wuta daga yan sandan, sai maharan suka ci na kare.

Ya bayyana Adeniji Sakiru mai shekaru 32 a matsayin wanda aka kama a yayin harin.

Oyeyemi ya ci gaba da cewa:

"Abun bakin ciki, wani Dayo Bankole, dan kasuwa a kasuwar, wanda yan fashin suka harba ya kwanta dama yayin da yake samun kulawar likitoci a babban asibitin Ijaye da ke Abeokuta."

Ya kuma bayyana cewa kwamishina mai barin gado, Frank Mba ya yi umurnin tura mai laifin da aka kama zuwa sashin binciken laifuka don ci gaba da bincike, rahoton The Cable.

Ya ce Mba, wanda ya kasance AIG a yanzu ya kuma yi umurnin kamo sauran masu laifin tare da gurfanar da su.

Ya roki asibitoci da su sanar da yan sanda idan suka ga wani da raunin harbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN