1_ Idan Mace tana cikin Fushi, Mafi yawan abubuwan da take furtawa ba hakan take nufi ba
2_ Lokaci Mafi Muni ga Mace, shine Lokacin da Wanda ta bawa gabadaya zuciyarta ya gujeta
3_ Mace ba Kamar kayan sabulun talla bace, idan Kai baka Bata kulawa ba, to wani zai Bata
4_ Yana daukar lokaci kafin Mace ta Mika dukkan yardarta ga Da Namiji, sannan akwai Mutukar wahala idan ta amince da kai ta guje ka, Don Haka idan ka ci Amanarta, kawai ka manta da batun sake dawowa
5_ Ya Mace Kamar Makaranta take, domin bazaka taba kaiwa makurar da zakace ka daina kulata ba inhar da Rai da Lafiya
6_ Zata iya zamowa Mai Daci agareka a yanxu, Kuma ta zamo Mai Zaki agareka, yadai danganta da yanayin da kake tafiyar da ita
7_ Akwai mutukar wahala Mace ta Manta Abu, saidai tafi tuna lokutan da aka kuntata Mata, Don Haka ka daina kuntatawa Matarka/Budurwarka
8_ Mace tana iya zamowa mai mutukar Sirri, Mafi yawan Lokutan da suka karbi bacin rai wajen Da Namiji, sukan tafi gidajen kawayensu suyi kuka
9_ Mafi yawan Mata na bukatar Rarrashi, ta wannan fannin maza da yawa suna kwafsawa
10_ Mata suna da kamanceceniya da Gishiri, Lokacin da suke tare da Kai, Bai zama lallai kaga muhimmancinsu ba, amma rashinsu kansa komi ya dawo lami duk dukiyar da kake takama da ita
11_ Idan tana Sonka, zata iya Yi maka duk abinda ka bukata duk a domin ta Sanya zuciyarka cikin Farinciki. Don Haka kada ka takura ta Akan ta so ka
12_ Idan har da Gaske mace na sonka, duk karfin bukatarta, bazata taba Rokar ka kudi ba, sannan ba zata taba Bari ka dinga kashe Mata kudi akan wasu kananun bukatunta ba. Da wannan Halayya ne, suke bambamta kansu da sauran Mata
Dan uwa, idan har ka samu Mace Mai sonka da Gaskiya, Mai tarbiyya, Mai Kamun Kai, da Girmama mutane. Ajiye batun kyau a gefe, kada ka kuskura ta Kufce maka
ALLAH YA HADA KOWA DA ABOKAN ZAMA NAGARI
Credit: Kano Online TV
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI