Hukumar Hisbah a jihar Kebbi ta cafke wasu samari da Yan Mata a wani gidan baki a garin Birnin kebbi bisa zargin laifin cudanya da ma'amala da ya saba wa dokokin addinin Musulunci.
Kwamandan Hisbah na jihar Kebbi Ustaz Sulaiman Muhammad ya shaida wa manema labarai a garin Birnin kebbi ranar Talata 25 ga watan Afrilu 2023. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.
Ya ce jami'an hukumar sun kai samame a wani gidan baki da dare a garin Birnin kebbi inda suka cafke wadannan matasan da suka hada da maza bakwai tare da Mata hudu ranar Litinin 24 ga watan Afrilu 2023.
Sulaiman ya yi kira ga iyayen samari da Yan Mata su kula da tarbiyyar yayansu, su kuma sa ido sosai kan maamalar yayansu.
Bayan gudanar da bincike, hukumar ta gargadi samarin da Yan matan a gaban iyayensu da hukumar ta gagyata aka gudanar da bincike a gabansu. Ta bukaci su zama matasa na gari masu bin dokokin addini.
Hukumar ta mika samarin da Yan mata ga iyayensu bayan an cika takardun alkawarin cewa samarin da Yan mata za su zama masu kiyaye dokokin addini, tare da guje wa aikata alfasha.
BY ISYAKU.COM