Kotun Majistiri da ke gidan Murtala a Kano ta umarci wani mutum Isyaku Shu'aibu da ke unguwar Ja'en ya yanka Zakaransa. Dala FM Kano ta wallafa.
Maƙocinsa Malam Yusuf Muhammad Ja'en ne ya shigar da ƙara Kotun kan cewa Zakaran yana shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci da yawan Cara.
Amma koda aka karantowa wanda ake ƙara ya ce, gaskiya ne Zakaran na yawan yin Cara kuma zai yanka shi ne a bikin "Good Friday" don haka ya roƙi Kotun da ta sahale masa zuwa ranar.
Mai shari'a Halima Wali ta amince inda ta umarci ya killace Zakaran kuma ya yanka shi a Jumu'a mai zuwa wato ranar "Good Friday" É—in.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI