A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu daga cikin iyalan Hakimin kauyen Nasarawa a karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.
An yi garkuwa da matarsa Halima Kabiru mai shekaru 38 da dansa Dahiru Kabiru mai shekaru 20. PM News ta rahotu.
Mista Mamman Dauda, kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da yin garkuwa da mutanen.
“A ranar 2 ga Afrilu, da misalin karfe 12:45 na darr, mun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga bakwai sun kai farmaki gidan hakimin kauyen Nasarawa inda suka yi garkuwa da matarsa da dansa.
“Masu garkuwan sun kai wadanda aka sace zuwa inda ba a san inda suke ba. Bayan samun bayanin, nan da nan muka kafa tawagar ceto a sassan da ke makwabtaka da su. A yayin da muke magana, tawagar tana aiki tukuru don ceto wadanda lamarin ya shafa ba tare da sun ji rauni ba,” inji shi.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa za a kubutar da wadanda aka sace tare da kama wadanda suka yi garkuwa da su.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI