Sashen kula da korafin kwastomomi na CBN mai adireshin imel cpd@cbn.gov.ng ya cika makil da tarin korafe-korafe daga kwastomomi.
Duk da ana tsammanin CPD ya iya magance matsalolin kudi na kwastomomin bankuna, amma alamu sun nuna matsalar na ci gaba da ci kamar wuta da daji. Legit ya wallafa.
Korafe-korafen mutane dai ya fara daga matsalar cire kudi ta ATM, cire musu kudi ba tare da ka’ida ba da kuma wadanda suka tura kudi basu shiga ba
Ka’idar tura wa CBN korafi
Ana shawartar kwastomomin bankuna cewa, idan suka gaza samun hanyar warware matsala a bankunansu, su tura sakon korafi ga CBN ta akwatin imel din CPD.
A baya, Legit.ng ta tattaro muku yadda mutum zai mika sakon korafi ga CBN idan ya gaza samun mafita daga bankinsa.
Sauyin kudi a Najeriya na daya daga cikin abubuwan da suka jawo matsaloli ga kwastomomi da masu mu’amala da bankuna a fadin kasar nan.
Hakazalika, karancin sabbin kudi da kuma yawaitar bukatuwa ga amfani da hanyoyi tura kudi daga asusu zuwa asusu ya sake sanya bankuna shiga matsi.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan kasar ke fama da karancin sabbin takardun kudi da aka sauya a shekarar da ta gabata.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI