Kaico: Attajiri dan kasuwa ya shiga matsala bayan ya yi wa mai karamin karfi duka da sanda har ya suma


Wani dan kasuwa mai suna Joseph Danladi wanda ke zaune a Abuja a ranar Talata ya gurfana a gaban wata kotun yankin Kado Grade I, Abuja bisa zarginsa da dukan wani Joshua Caleb da sanda har sai da ya suma
.

 Danladi, mazaunin Gilmore, Jahi, Abuja, ana tuhumarsa da yin mummunan rauni. PM News ta rahoto.

 Lauyan masu shigar da kara, Stanley Nwafoaku, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da kara, Stephen Johnson wanda ke zaune kusa da babban fadar, kauyen Kado, Abuja ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Life Camp a ranar 11 ga watan Maris.

 Nwafoaku ya ce wanda ake kara lokacin wata gardama ya dauki sanda ya lakada wa Caleb duka har sai da ya suma aka garzaya da shi babban asibitin Gwarinpa kafin ya farfado bayan wasu sa’o’i.

 Mai gabatar da kara ya ce a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike, an kama wanda ake kara tare da tsare shi tare da wani Mansur Adamu wanda ya yi wa wanda ake kara naushi a fuska a fada tsakanin wanda ake kara da Caleb.

 Ya ce yayin binciken ‘yan sanda kuma, wanda ake tuhuma ya amsa laifin aikata laifin

 Laifin a cewarsa ya sabawa tanadin sashe na 245 da na 167 na kundin laifuffuka.

 Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

 Alkalin kotun, Muhammed Wakili ya bayar da belins Wanda aka yi kara a kan kudi N200,000 da kuma wanda zai tsaya masa.

 Wakili ya kuma dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 19 ga watan Mayu

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN