Ɗaya daga cikin na gaba-gaba wajen neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Muktar Betera Aliyu, ya ziyarci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu domin neman goyon bayan sa. Legit ya wallafa.
ÆŠan majalisar wakilan mai wakiltar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar a majalisar wakilai, na ci gaba da neman samun goyon baya a muradin sa na zama kakakin majalisar wakilai ta tarayya ta 10, cewar rahoton Tribune.
Zaɓaɓɓun ƴan majalisa, tsofaffin ƴan majalisa da masu ruwa da tsaki na ta nuna goyon bayan su ga ɗan majalisar, wanda suka bayyana a matsayin mutumin mutane ne.
Neman goyon bayan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da Betara ya je, na daga cikin yaƙin neman ɗarewa kan kujerar da ya ke ta yi tun watanni uku da suka gabata, kafin zuwan ranar rantsar da sabuwar majalisar wakilai a watan Yuni.
A cikin wani faifan bidiyo da ofishin watsa labarai na ɗan majalisar suka fitar, Tinubi da kansa ya riƙe hannun Betara ya yin da ya yi masa iso zuwa cikin ɗaki domin tattaunawa, cewar rahoton Vanguard
Ziyarar da hon. Betera ya kai ta neman goyon bayan wajen Tinubu, ya yi ta ne a sabon mazaunin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da ke a gidan tsaro na ƙasa a birnin tarayya Abuja, bayan Tinubu ya dawo daga Umrah.
Waɗanda aka nuna a cikin bidiyon tare da Betara sun haɗa da shugaban majalisar dattawa mai barin gado, Sanata Ahmad Lawan, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi da kuma sauran wasu na kusa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI