Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar da cikon zaben gwamnoni a yau Asabar, 15 ga watan Afrilu a jihohin Adamawa da Kebbi. Wannan ya biyo bayan ayyana zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris da aka yi a matsayin wanda bai kammlu ba a jihohin.
Hakazalika, hukumar zaben za ta gudanar da cikon zabe na kujerun yan majalisun jiha da na tarayya 94. Legit ya wallafa.
Ku ci gaba da bibiyarmu don kawo maku yadda zaben ke gudana kai tsaye
Manyan yan takara da kallo ke kansu a cikon zaben gwamnoni
Ahmadu Fintiri
Gwamnan jihar Adamawa kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Aisha Dahiru
Sanata kuma yar takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.
Nasiru Idris
Dan takarar gwamnan APC a jihar Kebbi wanda ke kan gaba kafin a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Janar Aminu Bande
Dan takarar gwamnan PDP a jihar Kebbi. Ana sa ran zaben cikon zai zamo tsakanin Bande da Idris.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI