Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, 13 ga Afrilu, 2023.
Maganar tana gaban ‘yan sanda kuma wanda ake zargin yana stsate a hannun ‘yan sanda.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya yi kokarin diban ruwan zafi domin yin wanka, bayan ya dawo gida daga kasuwar Igbudu inda yake yankan nama da sayar da nama.
Sai dai kuma an ce matarsa ta roke shi da kada ya taba ruwan. Ta ce ba ya ba su kudin siyan iskar gas balle kudin kula da gida.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya yi biris da matarsa, sannan ya tafi kai tsaye ya kunna iskar gas domin dumama ruwan zafi.
Rikici ya barke tsakanin ma’auratan wanda ya kai ga wanda ake zargin ya yi ta daba wa matarsa wuka har sai da ta fadi.
A lokacin ne wanda ake zargin ya garzaya da matarsa wani asibiti mai zaman kansa domin yi mata magani inda ta rasu.
Cike da radadin lamarin ya sa ‘yar tasa ta garzaya ofishin ‘yan sanda ta kai rahoton lamarin kuma nan take aka cafke wanda ake zargin.
BY ISYAKU.COM