Jagaba Ba Za Ka Shiga Villa Ba: Kotu Ta Hana Belin Mai Zanga-Zangar Kin Jinin Rantsar Da Tinubu


Wata kotun majistare da ke zama a yankin Zuba ta birnin tarayya, Abuja, ta ki bayar da belin fasinjan jirgin sama da ya yi zanga-zangar cewa ba za a rantsar da Tinubu ba a yan makonni da suka gabata.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kotun ta mika Obiajuli Uja, wanda ya yi furucin mai matukar jan hankali game da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, a cikin jirgin sama da zai tashi daga Abuja zuwa Lagas ga yan sanda. Legit ya wallafa.

Alkali Mohammed Abdulazeez Ismail ya zartar da hukunci

Da yake zartar da hukunci a kan bukatar neman belin da lauyan Uja ya gabatar, alkalin kotun, Mohammed Abdulazeez Ismail, ya bayyana cewa bukatar ya yi wuri da yawa.

A cewar alkalin, abubuwan da aka gabatar tare da bukatar Uja bai nuna cewa wanda ake karar bai da lafiyar da zai iya fuskantar shari'a ba illa ya nuna cewa zuciyarsa bata da nutsuwa sosai.

Ismail ya bayyana cewa koda dai kundin tsarin mulki ya bai wa kowani dan Najeriya yanci, kotu na da ikon hana mutum yancinsa bisa dalilai na lafiya, rahoton The Sun.

Da yake nuni ga tanadin sashi 35(1)(e) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara ta) da sashi 278 na dokar laifi (ACJA), 2015, alkalin kotun ya ce ba za a iya ba Uja beli ba.

Ya riki cewa a inda lafiyar kwakwalwar wanda ake kara ya zama matsala, kotun ke da alhakin tabbatar da yanayin lafiyar wanda ake karar.

Don haka ya ki bayar da belin mutumin sannan ya umurci a garkame Uja a gidan gyara halin Kuje.

Ya kuma yi umurnin cewa shugaban cibiyar ya dauki wanda ake karar zuwa wani asibitin gwamnati don tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa.

Daga nan sai ya dage shari'ar har zuwa 20 ga watan Afrilu don ci gaba da sauraronsa.

Ba za a rantsar da Tinubu ba, magoyin bayan Peter Obi ya yi zanga-zanga

A baya mun kawo cewa wani mutum ya kawo tsaiko yayin da wani jirgin sama ke gab da tashi daga Abuja zuwa Lagas inda ya ce sam ba za a rantsar da Bola Tinubu ba a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN