Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta amince da tsarin kato bayan ƙato wajen gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar gwamna a jihar Kogi. Legit ya wallafa.
Punch tace matakin sauya tsarin zaben daga amfani da Deleget zuwa zaɓen Kato bayan kato na kunshe ne a wata wasiƙa da muƙaddashin shugaban APC, Sanata Abubakar Kyari, ya rubuta.
Wasikar mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Afrilu, an rubuta ta domin sanar da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) matakin da jam'iyyar APC ta ɗauka.
Ku saurari karin bayani...
BY ISYAKU.COM