Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta saki motoci 67, babura uku da ta kwace daga hannun wasu ‘yan Shi’a a shekarar 2015. PM News ya rahoto.
Wannan dai ya kasance daidai da hukuncin da kotu ta yanke kan karar da aka shigar a ranar 15 ga watan Disamba 2021,
Wadanda suka shigar da kara (Mohammed-Auwal Yakubu da wasu 77) 'yan kungiyar Shi'a ne suka shigar da takardar sammaci ga Kwamishinan 'yan sanda da kuma Babban Lauyan Jihar Kaduna.
A ranar 9 ga watan Nuwamba, 2022, Mai shari’a Amina Bello ta babbar kotun jihar Kaduna ta yanke hukunci .
Bayan samun hukuncin, an ba da umarnin kotu ga kwamishinan ‘yan sanda wanda shi ne wanda ake tuhuma na farko a shari’ar,” inji shi.
Sai dai jami’in ‘yan sandan da ya sa ido kan sakin motocin ga masu shigar da kara, ya ki cewa komai kan lamarin, yana mai jaddada cewa ba shi da ikon yin hakan.
BY ISYAKU.COM