Allah kadai ne zai hana a rantsar da Tinubu, ba wani Gwamnatin wucin-gadi - Malamin addini ya magantu


Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya ce ba za a samu gwamnatin rikon kwarya a Najeriya ba kuma babu abin da zai hana bikin rantsar da Tinubu a Najeriya. PM News ta rahoto.

 A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu, Primate Ayodele ya bayyana cewa duk da kura-kurai a zaben, ba za a samu wani abu kamar gwamnatin wucin gadi ba domin Allah bai nuna masa komai ba.

 Ya bayyana cewa wasu Malaman addini na iya ganin gwamnatin rikon kwarya ko kuma canza sheka a bikin rantsar da Tinubu, amma shi abin da yake gani shi ne ranar ba za ta canza ba kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika wa Bola Tinubu Mulki.

 ‘’Duk da kura-kurai, ban ga wani abu da zai hana rantsar da Tinubu ko wani abu kamar gwamnatin wucin gadi ba.  Ban san daga ina wannan ya fito ba amma wasu na iya cewa suna gani, muna da Malaman addini masu fassarar kalmar Allah daban-daban amma daga hange na, ranar rantsar da Tinubu za ta tabbata.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN