Kai tsaye: 'Yan APC da PDP sun kaure da kazamar fada a wata jiha, an harbi wani mutum


Wani mutum ya samu mummunan raunin harbin bindiga a lokacin da magoya bayan jam’iyyar APC da PDP suka kaure da fada a Fatakwal ta jihar Ribas a ranar Litinin
.

A tun farko, wasu magoya bayan PDP sun yi zanga-zanga a gaban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta da ke hanyar Aba a birnin na Fatakwal. Rahotun legit.

Masu zanga-zangar na neman a yi zaman gaba-gadi don duba tare da bincike kan kayayyakin aikin zabe da dukkan jam’iyyun siyasa.

APC za ta dumfari ofishin INEC
Jam’iyyar APC, karkashin jagorancin dan takararta na gwamna a jihar, Tonye Cole a ranar Juma’ar da ta gabata ta ce za ta fito don mika kokenta a ofishin hukumar zabe ta INEC.

A cewar Cole, za a mamaye ofishin na INEC ne domin tabbatar da an saki sahihan takardun aikin zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris don ba APC damar shigar da karar kalubalantar zaben.

Dan jaridar Punch da ke wurin da kitimurmurar ke faruwa ya ce, yayin da ‘yan PDP ke zanga-zanga, Cole da shugaban APC na jihar, Emeka Beke da sauran ‘yan APC sun bayyana a ofishin na INEC.

Matasan da ke zanga-zanga sun dumfari inda suke, inda suka yi ta jifan Cole da ‘yan tawgaarsa ta 'yan APC.

Yadda aka tafi da Cole, 'yan PDP na jifa
Wasu jami’an tsaron da ke tare da Cole sun tafi dashi a mota, inda ‘yan zanga-zangar PDP suka ci gaba da jifa da ledojin ruwa da duwatsu, Within Nigeria ta ruwaito.

Cikin kankanin lokaci, sojojin 6 Division, ‘yan sanda da jami’an NSCDC suka iso wurin tare da fara harbin iska don watsa masu zanga-zangar.

Sai dai, wani ganau ya shaida cewa, wani jami’in tsaro da ke tare da Cole ya harbi wani daga cikin masu zanga-zangar da ya yi ta kansa.

An ruwaito cewa, ya samu mummunan raunin da yasa ya kwanta a kasa kafin daga bisani abokansa suka dauke shi.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu wani bayani na yadda aka shawo kan lamarin ba da kuma halin da wanda ya samu raunin ke ciki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN