Gwamnati ta ayyana Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu don bukukuwan Easter


Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin, 7 da 10 ga watan Afrilu a matsayin hutu albarkacin bukukuwan Easter da Kiristoci za su yi a fadin Najeriya
.

Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore, ya fitar a Abuja ranar Laraba. Aminiya ta rahoto.

Ya bukaci mabiya addinin na Kirista da su yi amfani da lokacin wajen kwaikwayon halayen sadaukarwa, kaunar juna, yafiya, soyayya, hakuri da zaman lafiya da Annabi Isah (A.S) ya koyar.

Ministan ya kuma bukace su da su yi amfani da lokacin wajen yi wa Najeriya addu’o’i na musamman saboda kalubalen tsaron da take fama da su.

“Tsaro sha’ani ne da ya shafi kowa. Saboda haka, nake kira ga ’yan Najeriya da ma ’yan kasar waje mazauna kasarmu da su ci gaba da nuna halin kishin kasa ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan kasa,” in ji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati na yin duk kokarinta wajen ganin an mika mulki lami lafiya bayan kammala zaben sabuwar gwamnat

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN