Misis Aigbe ta bayyana hakan ne a wata lacca/ addu’o’i na musamman da ita da mijinta, Kazeem Adeoti suka shirya a ranar Asabar. Dailynigerian ya rahoto.
Jarumar wadda ta kuma bayyana cewa sabon sunanta yanzu shine Meenah.
A wani faifan bidiyo na taron wanda ya fito a ranar Lahadi, jarumar ta ce, “Insha Allahu, sabon sunana shi ne Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah da H."
Ta kuma nuna jin dadin ta ga bakin da suka halarci laccar.
Jarumar dai ta auri Mista Adeoti ne a shekarar 2022 kuma an zarge ta da aikata ba daidai ba yayin da take aure da tsohon mijinta ta, Lanre Gentry.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI