Jerin Sunayen Gwamnonin da Suka Fara Takun Saƙa da Waɗanda Zasu Gaje Su Tun Kafin Miƙa Mulki


Wasu gwamnonin jihohi sun sha kashi a hannun manyan abokan hamayyarsu a zaben gwamnoni da mambobin majalisun jihohi da aka kammala ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Gwamnonin da hakan ta faru da su sun gama zangon mulki biyu na tsawon shekaru 8, amma duk da haka suka gaza samun amincewar mutanensu wajen tabbatar da ɗan takarar da suke so ya gaje su. Legit ya wallafa.

Bayan shan kashi a zaɓen da ya gabata, gwamnonin sun fara samun matsala da zababb


un da zasu gaje su har an fara cece-kuce da nuna yatsa.

Mafi yawan matsalolin da ke haɗa gwamnoni masu ci da masu jiran gadon sun shafi yanayin tafiyar da harkokin kuɗi na jihohi da wasu muhimman batutuwa.

Wasu daga cikin gwamnonin da muka tattaro muku sun ƙunshi, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Samuel Ortom na jihar Benuwai da Okezie Ikpeazu na Abiya.

Gwamna Ortom na jihar Benuwai
Gwamna mai barin gado a jihar Benuwai, Samuel Ortom, na PDP ya fara fuskantar ƙalubale daga zababben gwamna mai jiran gado, Hyacinth Aliya, na APC, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Manyan mutanen biyu sun fara nuna wa juna yatsa ne bayan wani kundi ya sulalo ya fito wanda zaɓaɓɓen gwamna ya aike wa shugaban kamfanin zuba hannun jari na Benuwai (BIPC), Alex Adum.

Gwamna Ikpeazu na Abiya
Gwamna mai barin gado na jam'iyyar PDP a Abiya, Okezie Ikpeazu, yanzu haka ya fara takun saƙa da zababben gwamna na Labour Party, Alex Otti, ya gargaɗi ya daina sa baki a gwamnatinsa.

A makon da ya shige, babbar kotun tarayya a Abuja ta garkame wasu asusunan banki mallakin jihar, lamarin da gwamna Ikpeazu ya zargi Otti da kulla manaƙisa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN