Gabanin saukar Buhari daga mulki, Aisha ta yi wa Tinubu wani fata mai cike da tausayi ana cikin bikin karamar Sallah


Uwargidan shugaban kasa, Misis Aisha Buhari, ta bayyana godiyarta ga daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon baya da addu’o’in da suka ba gwamnatin maigidanta, shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin shekaru takwas da suka gabata.

 Buhari zai mika wa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 bayan shafe shekaru takwas yana mulki. PM News ya rahoto.

 Tinubu, wanda kuma dan jam’iyyar All Progressives Congress, APC ne kamar shugaban kasa mai barin gado ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

 Uwargidan shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na ofishinta, Mista Suleiman Haruna, ya fitar a ranar Juma’a bayan kammala Sallar Eid-el-Fitr a Abuja.  Ya kuma yi fatan gwamnatin Tinubu mai jiran gado ta samu zaman lafiya da nasara.

 Ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’o’in samun dauwamammen zaman lafiya da tsaro a kasar.

 Uwargidan shugaban kasa ta samu halartar uwargidan babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Hajara Alkali Baba da sauran ‘yan uwa domin gudanar da Sallar Eid-el-Fitr a Abuja.

 Asiha Buhari ta bukaci al’ummar musulmi da su yi tunani a kan kyawawan darussa na watan Ramadan.

 Yayin da take yiwa ‘yan Najeriya fatan bukukuwan Sallah lafiya, ta bukace su da su mika kyawawan halaye na rabawa, soyayya, goyon baya, gafara da sadaukarwa domin ci gaban bil’adama.

 Sanarwar ta ruwaito mataimakin limamin masallacin fadar gwamnati, Sheikh Musa Dantsoho, yana kira ga al’ummar musulmi da su yi koyi da darussan watan Ramadan da suka hada da soyayya, sadaukarwa, hakuri da kuma tsoron Allah.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN