Ana ci gaba da cece-kuce game da lafiyar zababben shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, inda ake cewa a halin yanzu yana karbar kulawar asibiti.
Sai dai, sanata Orji Uzor Kalu ya yi watsi da duk wata jita-jita da ake yadawa, inda yace lafiyar Tinubu lau kuma ba a kwance yake a gadon asibiti ba. Legit Hausa ya wallafa.
Kalu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a bikin cikarsa shekaru 63 a Abuja, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.
Bayanan da Kalu ya yi game da lafiyar Tinubu
A cewarsa:
“Zababben shugaban kasanmu lafiyarsa kalau. Ba gaskiya bane cewa bashi da lafiya. Bana son magana da yawa. Yana cikin koshin lafiya; yana cikin taitayinsa.”
Hakazalika, ya tuna da wata tattaunawa da ya yi da wani abokinsa game da lafiyar Bola Tinubu, Daily Post ta ruwaito.
Ya kara da cewa:
“Wani abokin aiki na jiya ya ce ya ji labarin wai zababben shugaban kasa Tinubu na kwance a asibiti.
“Na shaida lafiyar shugaban kasa mai jiran gado kalau ba ya kwance a asibiti; ba gaskiya bane cewa yana kwance a asibiti.
Mun yi musu. Na fada masa zababben shugaban kasa lafiyarsa lau.”
Yadda aka fara yada jita-jita game da Tinubu
A ranar 22 ga watan Mayun 2023 ne aka fara yada labarin jita-jita cewa Tinubu ya fece kasar waje domin neman magani a rashin lafiyar da yake fama dashi.
Ana zargin cewa, Tinubu ya kwanta rashin lafiya bayan shafe watanni yana kamfen din takarar shugaban kasa a shekarar nan.
Sai dai, tawagarsa ta yada labarai ta gaggauta yin watsi da rahotannin, inda suka ce Tinubun ya tafi Landan da Faris ne domin shakatawa da hutawa.
A bangare guda, shugaban kasa Ukraine ya taya Tinubu murnar lashe zabe, kana ya gayyace shi zuwa kasarsa domin tattauna wasu bayanai.
BY ISYAKU.COM