Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu ta tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da wasu shida suka tsira daga hatsarin kwale-kwale a Dam Kanwa da ke karamar hukumar Madobi a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce wani Umar Faruk-Dalada ne ya kai rahoton faruwar lamarin, sannan ya kuma bayar da sunayen wadanda abin ya shafa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
"Al'amarin ya faru ne a ranar 22 ga Afrilu, da misalin karfe 5:40 na yamma," in ji shi.
“Akwai mutane 11 a cikin kwale-kwalen, an ceto shida da ransu, yayin da aka ceto biyar a cikin sumamme.
“Sunayen wadanda suka rasa rayukansu a cikin hatsarin sune Abdulrazak Nabara, mai shekaru 40; Dalha Muktar-Atamma, 40; Mustapha Ibrahim, 45; Umar Isah mai shekaru 35 da Umar Idris mai shekaru 35.”
PRO ya ce wadanda abin ya shafa sun fito ne daga karamar hukumar Fagge da ke jihar.
Ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan hatsarin kuma za a bayyana sakamakon binciken idan an kammala.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI