Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Hajiya Saratu Umar a matsayin babbar sakatariyar hukumar bunkasa zuba jari ta Najeriya NIPC, nan take.
Mista Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
A cikin umarnin da shugaba Buhari ya ba wa Ministan Masana'antu, Ciniki da Zuba Jari, Richard Adebayo, shugaban ya kuma umurci babban Darakta a Hukumar da ya karbi ragamar aiki cikin gaggawa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a watan Yulin 2022 Buhari ya amince da nadin Hajiya Saratu Umar a matsayin babbar sakatariyar hukumar NIPC na tsawon shekaru biyar.
An fara nada Saratu a matsayin a watan Yulin 2014.
BY ISYAKU.COM