Onje Gye-Wado wanda ya taba zama Mataimakin Gwamna a jihar Nasarawa, ya samu kan shi a hannun ‘yan bindiga masu yin garkuwa.
Rahoton da Punch ta fitar a safiyar nan ya tabbatar da miyagun ‘yan bindiga sun dauke Farfesa Onje Gye-Wado a yankinsa na Gwagi da ke garin Wamba. Legit ya rahoto.
Wani daga cikin ‘yanuwan Onje Gye-Wado ya shaidawa manema labarai cewa a daren Juma’a ‘yan bindigan su ka hauro katanga, suka shigo masa gida.
Miyagun sun fasa tagar dakin mai dakin Farfesa Onje Gye-Wado ne, har su ka samu damar kai gare shi, daga nan su ka tsere da shi zuwa inda ba a sani ba.
Bayanin 'Danuwan Gye-Wado
Mai dakinsa ta zo gida domin bikin Easter, sai su ka shigo cikin gidan ta tagar dakinta, su ka dauke shi zuwa wani boyayyen wuri.
Mu na masa fatan jami’an tsaro za su yi kokarin ceto shi ba tare da wani abu ya same shi ba.
- Wata majiya
Jaridar nan ta Vanguard ta tabbatar da Onje Gye-Wado wanda ya yi mulki tsakanin 1999 da 2003 ya taba sha da kyar a hannun masu neman dauke shi.
Gye-Wado ya yi mataimakin Gwamna ne a lokacin da Abdullahi Adamu yake mulki a Nasarawa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na reshen Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel ya tabbatar da labarin garkuwa da dattijon, ya ce su na kokarin kubutar da shi.
DSP Nansel yake cewa mummunnan labarin ya zo masu da kusan karfe 12:30 na dare cewa ‘yan bindiga sun shiga gidan Gye-wado da yake Kauyen Gwagi.
Da jin labarin, jami’an ‘yan sanda da ke karamar hukumar Wamba su ka shiga bakin aiki, amma kafin su yi wani yunkuri, ‘yan bindigan sun yi gaba da shi.
BY ISYAKU.COM