Type Here to Get Search Results !

Main event

Bidiyo: Yadda Mage Ta Yi Tsalle Ta Faɗa Kan Liman Yayin Da Yake Jan Sallah


Mage (mace) ko kuma Muzuru (namiji) na daga cikin dabbobin da mutane da yawa suka aminta dasu har suke ajiyewa a gidajensu domin debe musu kewa. 

Sai dai, duk da haka har yanzu akwai wasu mutane dake matukar tsoron mage, wasu ko gidan da ake kiwon mage basa iya ziyarta saboda tsananin tsoron mage. Legit ya wallafa.

Koda mutum baya jin tsoron dabbobin da ake ajiyewa a gida, a mafi yawan lokuta mutum kan razana tare da firgita idan irin wadannan dabbobi suka fado kansa ko kuma suka yi motsi ko kuka babu zato babu tsammani.

Sabanin irin wadannan mutane dake razana ko firgita idan dabbobin da suke kiwo sun fado kansu ko sun yi kuka babu tsammani, Limamin Masallacin Abubakr al Siddiq da ke birnin Bordj Bou Arreridj da ke kasar Algeria ya bawa mutane mamaki saboda jarumtarsa.

Ko gezau limamin bai yi ba a yayin da wata mage ta daka tsalle ta fado kansa a yayin da yake cikin rera kira’ar Alqur’ani mai girma a lokacin da yake jan jama’a sallah.

A faifan bidiyon da shafin watsa labarai na TRT da ke kasar Turkiyya ta wallafa a shafinta na Tuwita (@trtafrikaHA) za’a iya ganin yadda magen ta yi tsalle ta haye kan kafadar Malam Liman kafin daga bisani ta hau tsakiyar kansa tare da gangarowa zuwa kan kirjinsa.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies