Farfesa Wole Soyinka, ya ce manufar sake fasalin naira ta kawar da babban bangare na nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu, inda ya kara da cewa shugaban na barin ofis ne cikin yanayin rashin jin dadi.
Ya ce manufar ta talauta ‘yan Najeriya tare da yin watsi da abubuwan alheri da gwamnatin Buhari ke fatan ta bari. Daily trust ta rahoto.
Soyinka ya yi magana a ranar Laraba yayin wata hira da Arise TV a shirin sa na safe.
Ya yaba wa wasu gwamnonin jihohin da suka kalubalanci manufofin gwamnatin tarayya a kotun, yana mai bayyana hakan a matsayin tsarin tarayya na gaskiya a aikace.
Soyinka ya ce, “To, ba na jin ko da muna bukatar mu yi amfani da karfin hankali wajen tantance mulkin Buhari saboda yana rayuwa ne a kan abin da bai dace ba.
“Ina magana ne kan manufofinsa, wanda, cikin dare daya, ya talauta miliyoyin ‘yan Nijeriya. Idan ya kasance yana fatan kasancewa kan babban matsayi, na yi hakuri, zai ji takaicin cewa matakin daya yi ya kawar da babban bangare na nasarorin da ya samu."
Ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da labaran karya, kamar yadda ya musanta wasu rubuce-rubucen da aka danganta masa a shafukan sada zumunta.
Soyinka ya sanar da bayar da tukuicin dala 1,000 ga duk wanda zai taimaka masa wajen gano wadanda suka rubuta wadannan rubuce-rubucen na bogi, ana alakanta shi da shi.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI