Wani basarake mai daraja ta uku a jihar Taraba, Kwe Ando Madugu, ya tsallake rijiya da baya a karamar hukumar Ussa bayan wasu matasa sun farmake shi tare da kona fadarsa da motoci.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matasan sun yi wa basaraken dukan kawo wuka sannan suka ji masa rauni yayin da suka cinna wuta a fadarsa.
An tattaro cewa matasan sun farmaki fadar Kwe Ando Madugu a ranar Litinin bayan ya ki bin umurninsu na neman a fatattaki makiyaya da zaune a yankin. Legit ya wallafa.
Suna dai zargin makiyayan da kasancewa da hannu a kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a wannan yanki.
Matasan sun zargi basaraken da hada kai da makiyayan. Kuma a yanzu haka yana kwance a asibiti an ba shi gado.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, wanda ya tabbatar da farmakin da aka kai wa basaraken ya ce ana gudanar da bincike a yanzu haka, rahoton Aminiya.
BY ISYAKU.COM