Gwamnatin jihar Delta karkashin jagorancin gwamna Ifeanyi Okowa ta sallami manyan hadimai 6 daga bakin aiki kan wasu halayen rashi'a É—a'a da suka yi a bainar jama'a. Legit Hausa ya wallafa.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa wannan matakin na kunshe ne a wata wasiƙa da Sakataren gwamnatin jihar, Chief Patrick Ukah, ya aike wa babban mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa.
Wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Maris, 2023, ta ce an kori hadiman daga bakin aike ne bisa ɓanɓarma da rashin riƙe sirrin kudirorin gwamnati mai ci.
Haka zalika gwamnatin ta bayyana cewa matakin tunbuƙe su daga kan muƙamansu zai fara aiki ne daga ranar Asabar, 1 ga watan Afrili, 2023.
Karin bayani na nan tafe...
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI