Kiristoci da Musulmai sama da 50 sun gudanar da taron buda baki tare da hadin gwiwar mabiya addinai daban daban domin karfafa zaman lafiya a jihar Kaduna. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
Taron wanda ya gudana a Unguwar Rimi, Kaduna, ya gudana ne a karkashin kungiyar Conflict Mitigation and Management Regional Council (CMMRC) da Community Peace Observers (CPO), tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan jarida ta zaman lafiya (NPJ).
Suna aiki don inganta kyawawan dabi'u game da zaman lafiya a tsakanin kabilu da addinai daban-daban game da bukatar rungumar zaman lafiya da kuma yin aiki a matsayin Jakadun Hadin kai a yankuna daban-daban a kan shirin Community Initiatives don inganta zaman lafiya (CIPP) a cikin jihar.
Mista Samson Auta, ko’odinetan kungiyar Community Peace Action Network (CPAN), na cibiyar sulhu ta Interfaith (IMC), Kaduna, ya bayyana cewa makasudin haduwar mu shine mu hada kai da ‘yan uwa musulmi wajen buda baki a azumin watan Ramadan a Unguwar Rimi. Kaduna North”.
Taron kuma an yi shi ne domin jaddada muhimmancin karfafa zaman lafiya da kuma juriya na addini a tsakanin mabiya kungiyoyin addinai da kungiyoyi daban-daban na jihar.
Manyan Malaman addinin Musulunci da na Kirista da kungiyoyin mata da kungiyoyin matasa da masu rike da mukaman gargajiya da jami’an tsaro ne suka halarci taron.
Auta ya ce, buda baki na watan Ramadan yana ba da dama mai kyau na tunani, sadaukar da kai ga wanda ya halicci dukkan bil'adama kuma ya zama hanya ce ga Kiristoci da Musulmai don yin hulɗa, tattaunawa da musayar saƙon fatan alheri na zaman lafiya da haɗin kai a cikin ƙasa.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI