Tarihi: Yadda Aka Faro Tafsiri Cikin Watan Ramadan a Najeriya


Baya ga azumi, babu wata babbar shaidar da take nuna ana cikin watan Ramadan a Æ™asar Hausa kamar yawaitar tafsirin AlÆ™ur’ani Mai girma. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Kafafen yaÉ—a labarai irin su rediyo da talabijin har soke wasu shirye-shiryen suke yi saboda yawan karatuttukan tafisirin da suke kawowa a cikin watan.

Sai dai, ba haka lamarin yake ba a shekarun baya, kuma an sha fama kafin tafsiri ya zama ruwan dare a watan Ramadan.

Tun daga zuwan Musulunci har zamanin jihadi da na mulkin mallakar Turawa, malamai a Æ™asar Hausa ba sa yarda su yi tafsiri a cikin jama’a.

Sai dai su koyar da manyan É—alibansu a cikin gidajensu.

Abin da ya sa haka shi ne darajar da suke bai wa ilimin tafsiri a matsayinsa na mafi ƙololuwar ilimin addinin Musulunci.

Haka kuma malaman sukan ji tsoron cewa karatun tafsirin zai iya rikitar da jahilai da masu Æ™arancin ilimi ta hanyar haska saÉ“anin masana kan hukunce-hukuncen da al’umma suka yi riÆ™o da su.

Wannan ya sa ko tafsirin da ake yi a irin waɗannan makarantu ya taƙaita ne ga littafin Tafsirin Jalalaini na Jalalal Dini al-Mahalli da Jalalal Dini al-Suyuɗi.

Duk da yake a zamanin jihadi, Sheikh Abdullahin Gwandu ya rubuta littafin tafsiri mai suna Diya’ut Ta’awil, sannan ya taÆ™aita shi zuwa Kifayatu Du’afa’us Sudan, kuma ya mayar da shi waÆ™a mai taken Miftahut Tafsir, duk da haka malaman wannan yanki ba su saki Tafsirul Jalalayni ba.

Farkon Tafsirin Ramadan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ya yi wa Halifan Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass mubayi’a a 1937 lokacin da ya je aikin Hajji.

Kuma a 1945 Sheikh Ibrahim Inyass ya ziyarci Birnin Kano.

A nan ne ya haÉ—u da É—aliban Malam Muhammadu Salga wanda ya rasu a 1938.

ÆŠaliban sun haÉ—a da Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari da Sheikh Shehu Mai Hula da Sheikh Abu Bakr Atiku da Sheikh Umar Falke da Sheikh Sani Kafanga.

WaÉ—annan É—aliban ne suka bi shi Senegal suka yi tarbiyyar Tijjaniyya a wurinsa.

A nan suka gano Sheikh Inyass yana gudanar da Tafsiri a bainar jama’a cikin watan Ramadan.

A farkon shekarun 1950 É—aliban suka dawo suka kafa majalisan karatunsu a cikin Birnin Kano.

Kuma idan watan azumi ya zo sai su juye zuwa Tafsiri.

Karatun da ya fi fice a cikinsu shi ne na Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari wanda yake gabatarwa a ’Yan Mota da ke daura da Kasuwar Kurmi.

Shi ne ya fara amfani da lasifika wurin karatu sannan kuma ya yi mumbarin da yake zama a kai domin na nesa ya iya ganinsa.

Kuma ya Æ™ara yawan littattafan da yake tafsiri da su, inda yake amfani da Hashiyah Alal Jalalain na Ahmad As Sawi da Ruhul Bayan na Isma’ila Hakki da Zadul Maisur Fi Ilm at Tafsir na Ibn Jawziy.

Daga cikin ’yan Tijjaniyya mabiyan Sheikh Inyas har da Ciroman Kano, Alhaii Muhammadu Sanusi.

Shi ma duk watan Ramadan wani malami Gwani ÆŠahiru na yi masa karatu a gidansa.

Lokacin da aka fara bayyanar da karatun Tafsiri sai ya buƙaci Malam Mustapha Alƙalin Bichi ya riƙa yi musu tafsiri.

Bayan rasuwar Malam Mustapha sai Sheikh Nasiru Kabara ya maye gurbinsa.

A 1953 Ciroma Sanusi ya zama Sarkin Kano kuma tun daga azumin 1954 aka fara tafsirin Kur’ani a Fadar Sarkin Kano.

Daga nan karatun tafsiri ya yaɗu zuwa sauran garuruwan Hausawa musamman a ƙasashen Najeriya da Nijar.

Karatun Ƙur’ani a rediyo
A 1951 gwamnatin mulkin mallaka ta kafa gidan rediyon NBS a Legas tare da rassansa a Ibadan da Inugu da Kaduna.

Tun a 1932 dai aka fara sauraron rediyo a Najeriya bisa tsarin RDS, amma baki É—ayan shirye-shiryen na Ingilishi ne zalla.

Don haka aka kafa NBS saboda a fara gudanar da shirye-shirye a Najeriya kuma cikin harsunan ’yan Æ™asa.

Wannan gidan rediyo na NBS shi ne ya fara saka karatun AlÆ™ur’ani Mai girma a tasharsa da ke Kaduna.

Sai dai hakan ya jawo ce-ceku-ce. Domin kuwa Musulmi da ke Arewacin Najeriya sun koka da suka ji karatun Kur’ani a cikin na’ura ta ‘sharholiya’ irin rediyo wadda aka saba jin kaÉ—e-kaÉ—e da kuma zantuttukan duniya a cikinta.

Don haka suka yi ta rubuta wasiÆ™un Æ™orafi zuwa ga gidan rediyon inda suka buÆ™aci a daina sa Kur’ani saboda yin hakan tamkar wulaÆ™anta shi ne.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi shi ne Shugaban Hukumar Daraktocin Gidan Rediyon a wancan lokaci.

Don haka a wurinsa shugabannin gidan rediyon suka nemi mafita.

A 1954 Sarki Sanusi ya dakatar da saka karatun Kur’ani a rediyo, inda ya nemi fatawa daga malaman Tijjaniya na Kano da kuma Sarkin Zazzau Ja’afaru É—an Isiyaku, wanda shi ne wanda ake gani ya fi kowanne Sarki a Arewacin Najeriya ilimin addini a lokacin.

Malaman Kano sai suka aike da fatawar zuwa ga Shehinsu Ibrahim Inyass.

Amma sai baki ya rabu biyu. Shehi Inyas ya ba da fatawar cewa saka karatun Kur’ani a rediyo ya halatta yayin da Sarkin Zazzau Ja’afaru ya ce tunda yake babu wani nassi Æ™arara da ya bayyana halacci ko haramcin saka Kur’ani a rediyo, yana ganin gara kada a sa saboda kada a buÉ—e Æ™ofar keta alfarmar Littafi Mai girma.

Ganin an samu wannan saɓani sai ɗaliban Inyas na Kano suka tura masa da fatawar Sarkin Zazzau.

Daga nan ya rubuto littafi mai taken Al-Hujja al-Baligha fi Kaunil Iza’atil Kur’ani Sa’igha, inda a nan ya yi cikakken bayani tare da kawo gamsassun hujjoji cewa sa karatun Kur’ani a rediyo ko bai kai matsayin wajibi ba, ya kai matakin halal abin so.

Bayan samun wannan fatawar ce aka ci gaba da saka karatun AlÆ™ur’ani a rediyo.

Tafsiri a Rediyo
A 1962, Rediyon NBC Kaduna ya fara sa karatuttukan tafsiri na malamai da ake naÉ—a a kasakasai na rikoda.

Malaman sun haÉ—a da Modibbo Jilani Yola da Malam Baba Sakkwato da Malam Tijjani Usman Zangon Barebari da Malam Nasiru Kabara daga Kano.

Amma dai jefi-jefi ake sa wa kuma ba lallai sai cikin watan Ramadan ba.

Sai a 1967 ne aka fara saka karatun tafsiri cikin watan Ramadan a gidan rediyo na NBC Kaduna.

Karatun da aka fara sakawa shi ne wanda Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yake gudanarwa a Masallacin Sultan Bello.

SaÉ“anin sauran malaman da suke tafsiri, shi ba ya É—ariÆ™a, hasali ma babban aikin da ya sa gaba shi ne sukar aÆ™idun ’yan É—ariÆ™ar.

Koda yake tun 1962 yake gudanar da tafsiri a Masallacin Sultan Bello, lokacin da aka fara sa shi a rediyo sai ya fara sassautawa saboda a cewarsa babu damar amsa tambayoyin waÉ—anda ba su fahimce shi ba.

A 1967 ne kuma gwamnatin mulkin soja ta Janar Gowon ta ƙara jihohin Najeriya daga huɗu zuwa 12.

Don haka jihohi shidan da ke Arewa su ma kowace ta buÉ—e gidan rediyo sai ta samar da gurbin karatun Tafsiri.

Amma a Rediyon Najeriya Kaduna, wacce ita ake ji a duk faɗin Najeriya dama wasu daga cikin ƙasashen waje, Sheikh Abubakar Gumi ne kaɗai ke yin tafsiri tsawon shekara 10 daga 1967 zuwa 1977.

A cikin watan Maris na 1977 ne Æ™ungiyoyin ’yan DariÆ™ar Tijjaniya da suka haÉ—a da Fityanul Islam da Dakarun ÆŠan Fodiyo da Jama’atu Ahlis Sunnah suka gudanar da zanga-zanga a Birnin Kaduna inda suka roÆ™i gwamnati da gidan rediyon su dakatar da tafsirin Sheikh Abubakar Gumi.

Sakamakon haka Mataimakin Shugaban Kasa na mulkin Soji Manjo Janar Shehu Musa ’Yar’adua ya umarci gidan rediyon ya ci gaba da karatun Gumi amma ya bai wa wani malamin Tijjaniyya dama.

Don haka aka zaɓo Sheikh Umar Sanda Idris, mutumin Zariya mazaunin Kaduna ya cike wannan gurbi.

Ya kuma gudanar da tafisrin tsawon shekara uku daga 1977 zuwa 1979 amma a tsittsinke saboda a ranaku da yawa ma’aikatan rediyo kan ce ba za su samu kawo shirin ba saboda tangarÉ—ar na’ura.

Shi kuma salon karatunsa ba irin na rediyo ba ne. Irin dai wancan tafsirin ne na asali wanda malamai suke yi tsakaninsu da É—alibansu.

Domin kuwa a cikin watannin azumi guda uku bai kammala tafsirin Suratul Fatiha ba, saɓanin Sheikh Gumi da ke kammala ta cikin minti 20.

Wannan ya sa tafsirin bai ja hankalin masu sauraro ba.

Don haka Kungiyar Fityanul Islam sai ta sayi fili a rediyo aka fara saka karatun Sheikh Zubairu Surajo.

Shi kuma kafin watan ya ƙare sai ya tafi Umara inda ya bar Malam Mahmud Umar ya ci gaba.

Cikin ikon Allah sai karatun Malam Mahmud ya fi karɓuwa.

Don haka da Malam Zubair ya dawo daga Umara sai Malam Mahmoud ya ƙi sauka daga kujerar.

Wannan ya sa a 1979 aka gudanar da tafsiri guda huÉ—u a Rediyon Najeriya na Kaduna; Uku daga É“angaren Tijjaniya É—aya daga É“angaren Izala.

Bayan azumin aka samu sulhu a Tijjaniya inda aka É—auko Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda dama ana sa tafsirinsa a gidan rediyon Bauchi ya dawo Kaduna.

Nan take Malam Umar Sanda ya yi ritaya daga tafsirin rediyo amma Fityanu ba ta amince ba.

Don haka aka ci gaba da tafsirin Malam Mahmud Umar daga Masallacin Juma’a na Kano Road da Sheikh Dahiru Bauchi daga Masallacin Tudun Wada sai kuma Sheikh Abubakar Gumi daga Masallacin Sultan Bello.

Shi ma Sheikh Dahiru Bauchi yana cikin waÉ—ancan malamai ’yan Æ™ablu da suka yi karatu a Kaulaha wurin Sheikh Ibrahim Niasse tun cikin shekarun 1940.

Inda salon tafsirinsa ya bambanta da kowa shi ne ba ya duba wani littafi sai dai ya riƙe carbinsa.

Tun daga wancan lokaci É“angarorin biyu suke amfani da wajen tafsiri wurin sukar juna da mayar wa da juna martani.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN