Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki zaɓaɓɓen gwamna, Abba Kabir Yusuf, bisa kalaman da ya yi a baya-bayan nan kan ciyo bashi. Legit ya wallafawa.
Ganduje ya kira kalaman gwamna mai jiran gadon da, "Mara tushe" da kuma alama ce dake nuna bai san inda ya dosa ba, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya shawarci masu baiwa gwamnatin Ganduje Bashi su dakata kuma ya gargaÉ—i masu gini a filayen gwamnati su shiga taitayinsu.
Ganduje ya maida martani
Ganduje ya yi martani kan kalaman ne yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Asabar jim kaÉ—an bayan kammala taron Addu'o'i da rokon Allah ya taimaki shugaban masa mai jiran gado, Bola Tinubu.
Ya ce:
"Wannan babbar alama ce a zahiri da ke nuna shugabancinsu ba shi da manufa saboda irin waÉ—annan shawarin ba su da amfani kuma ba su da tushe."
"Yana magana da jiji da kai kamar yanzu haka shi ne gwamna Kano. Muna masa fatan ya yi abun kirki amma abinda muke so ka gane zamu kalubalanci wannan nasarar ta wucin gadi a Kotun sauraron karar zaɓe."
"Amma ka ga mutum ya fara magana barkatai irin waÉ—an nan, ai kai zaka wa kanka alkalancin cewa bai fara da kafar dama ba."
Abba Gida-Gida ya fara magana kan harkokin gwamnatin Kano mako ɗaya bayan INEC ta ce shi ne ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023, wanda Ganduje yace a haɗu a Kotu.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI