Matashiya ta haifi yara biyar, maza 3 mata 2, bayan shekara 8 bata haihu ba


Wata matashiya yar Najeriya wacce ta yi wa kasa hidima kwanan nan ta samu karuwar yara yan biyar.

Matar mai suna Chidimma Amaechi wacce ta fito daga jihar Ebonyi ta haifi yaran a Awka, babban birnin jihar Anambra. Legit Hausa ya wallafa.

A bisa wani labari da Okoye Ifeoma Obi, ya wallafa a Facebook, mai jegon ta haifi yaran shinkafa da wake wato maza uku da mata biyu.

Wannan gagarumin ni'ima da Chidimma ta samu yana zuwa ne bayan ta shafe shekaru takwas ba tare da haihuwa ba

Wani bangare na labarin ya ce:

"Mata na da karfi faaaaa. Yara biyar a lokaci daya. Ina rokon irin wannan, biyu kawai nake so. Wannan labari ne mai dadi da ya fito daga jihar Anambra. 

Ina taya Chidimma Amaechi wacce ta haifi yan biyar a Awka murnar wannan ni'ima na Ubangiji. Ta haifi maza 3 da mata 2 a asibitin Life Hospital Awka, jihar Anambra. Wannan ya cancanci ayi biki."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN