Za a kashe mutum 3 har Lahira sakamakon aikata kisan kai a Jigawa


Wata babbar kotu da ke Kaugama a Jihar Jigawa ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kisan kai da aikata fashi da makami.

Kotun dai ta sami Suleiman Bello da Auwalu Muhammed da kuma Yakubu Muhammed da laifin kashe wani mai suna Audu Saje, mazaunin kauyen Manda na Karamar Hukumar, sannan suka gudu da babur dinsa. Aminu ya rahoto.

Kazalika, kotun ta same su da laifin sace wata mata mai suna Hadiza Abdullahi ta garin Marma da ke Karamar Hukumar Kirikasamma, sannan suka nemi a biya su fansar Naira miliyan 150.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a M. M. Kaugama, ya ce masu shigar da kara, bisa jagorancin Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, Dokta, Musa Adamu Aliyu, sun gamsar da kotun cewa mutanen da ake zargi sun aikata laifukan.

Sai dai kotun ta saki tare da wanke mutum na biyu a cikin wadanda ake zargin, Ya’u Mai Hatsi daga dukkan zarge-zargen.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN