Kimanin daliban Najeriya 4,000 ne ke makale a kasar Sudan sakamakon rikicin da ake fama da shi a can, in ji jaridar Daily Trust.
Shugaban kungiyar daliban Najeriya, Sudan (NANSS), Abubakar Babangida, ne ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust.
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin Najeriyar ta ce tana ci gaba da tuntuba mataki na gaba kan batun kwashe 'yan Najeriya a Sudan.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga bukatar da daliban Najeriya a Sudan suka gabatar
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi fama da tashin bama-bamai da harbe-harbe a babban birnin kasar Sudan a ranar Alhamis yayin da fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun janar-janar guda biyu bai nuna alamun raguwa ba gabanin bukukuwan karshen watan Ramadan.
Sama da mutane 300 ne aka kashe tun bayan barkewar fadan a ranar Asabar tsakanin dakarun da ke biyayya ga Hafsan Sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar runduna ta Rapid Support Forces (RSF).
A zantawarsa da daya daga cikin ‘yan jarida a daren jiya, Babangida ya ce akwai dalibai ‘yan Najeriya sama da 10,000 da ke karatu a Sudan a halin yanzu.
Sai dai ya ce galibin su suna hutu ne, inda ya ce kusan 4,000 daga cikinsu ne aka bari a baya.
Ya ce daliban, galibinsu mata, sun makale ne a Sudan a halin yanzu.
Bayanai sun ce mahukuntan Najeriya na kokarin tsara yadda za ta kwashe sauran dalibai Yan Najeriya da suka makale a Sudan sakamakon barkewar fadan, musamman a Khartoum.
BY ISYAKU.COM