Fusatattun mutane sun yi wa direba ruwan duwatsu har Lahira ana cikin azumi


Wasu fusatattun mutane, a ranar Litinin din da ta gabata, sun jefe wani mutum mai shekaru 35 da duwatsu har lahira bisa zarginsa da kashe mutane biyu tare da raunata wasu shida a wani hatsarin da ya afku a hanyar Ijoka, Akure, babban birnin jihar Ondo.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

 Odunlani-Omisanya ya ce hatsarin ya hada da wata mota da babur na kasuwanci.

 “Akwai hatsarin da ya kai ga mutuwar wani direban babur, kuma maimakon mutanen da ke kusa su taimakawa, sai suka koma yin halin jahilci ta hanyar kashe matashin direban tare da kona motarsa,” inji ta.

 Kakakin ‘yan sandan ta ci gaba da cewa bqncin gaggawar da ‘yan sandan suka yi na isa wajen, da an kashe iyayen direban su ma.

 Ta ce iyayen ba su cikin abin hawa daya da dansu amma sun zo wurin ne kawai don ganin abin da ke faruwa.

 "A gaba daya, an tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da wasu shidan da suka samu raunuka a hadarin a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti," in ji PPRO.

 Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya tattaro cewa, ana zargin direban da kasancewa Dan damfarar yanar gizo ne wanda aka fi sani da ‘Yahoo boy’.

 An ce ya yi tukin ganganci inda ya kutsa cikin wasu babura ‘yan kasuwa kusan biyar dauke da fasinjoji a wurare daban-daban a Ijo Mimo ta tashar mota ta Lahadi zuwa hanyar Ijoka a Akure.

 Wani ganau da bai so a buga sunansa ba, ya ce mutane uku ne suka mutu nan take, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.

 “Direban motar Toyota, wanda bai samu wani rauni ba, yana kokarin tserewa daga wurin, kafin wasu matasa suka kama shi, suka yi masa dukan tsiya.

 “Fusatattun mutanen sun jefe shi har lahira, yayin da ’yan daba suka kona motar da yake ciki,” inji shi.

 Shaidan idon ya kara da cewa an kai wadanda suka samu raunuka zuwa wani asibiti da ke kusa, yayin da aka bar gawar direban a wurin.

 NAN ta ruwaito cewa mai magana da yawun ‘yan sanda bai tabbatar da ko direban dan damfaran yanar gizo ne ko a’a ba

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN