Sake zaben Kebbi: Rundunar Yan sandan jihar ta magantu, ta sanar da wani muhimmin lamari


Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta ce rundunar tare da sauran jami'an tsaro sun shirya tsaf domin samar da tsaro don gudanar da zaben da za a yi a ranar Asabar a kananan hukumomi 20 na jihar. Jaridar Daily trust ta ruwaito.

 Tun da farko kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi CP Lawal Abubakar Daura ya gargadi kwamandojin yankin, DPOs da sauran kwamandojin dabarun yaki da su nuna kwarewa sosai tare da bin ka’idojin da aka sabunta na rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da ke aikin zabe.

 Ya gargadi jami’an da su kasance masu zaman kansu da kuma lura da yadda suke gudanar da ayyukansu daidai da ’yancin dan Adam na masu son zaman lafiya a jihar Kebbi.

 Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana zaben gwamnan jihar Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba sakamakon gagarumin soke zaben da aka yi a kananan hukumomi 20 cikin 21 na jihar.

 Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Yusuf Sa’idu, ya ce jimillar wadanda suka yi rajistar zaben sun kai 2,032041 inda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri’u 388,258 yayin da jam’iyyar PDP ta samu 342,980, wanda ya bar bambancin  45,278.

 Ya ce, “A yayin da ake hada-hadar, mun dauki bayanan inda aka soke wasu sakamako a kananan hukumomi 20 daga cikin 21 na jihar, jimilla 91,829”.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya ce CP ya kuma bukaci manyan jami’an ‘yan sandan da su tabbatar da tsaro a duk wuraren da abin ya shafa da kuma wuraren tattara sakamakon zabe a fadin jihar ta hanyar tura ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da nufin Samar da tsaro a wuraten zabe.

 CP ya kuma umurci jami'ai da su aiwatar da tsauraran dokar hana zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 12 na  dare zuwa 6 na yamma a ranar zaben don tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN