"Kai hasararren mutum ne a siyasa tun 1993", Tinubu ya yi wa Atiku kaca-kaca a Kotu


Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya koka kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar suka shigar na soke zaben sa.

 Tinubu, a wata takaddama ta farko da ya shigar gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, PEPC, da ke Abuja, ya bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya tsaya takara da ya sha kaye a yunkurinsa na neman shugabancin kasar tun 1993.

 Tinubu ya ce: “Mai gabatar da kara na daya (Atiku) ya tsaya takara tare da shan kaye a zabukan shugaban kasa a Najeriya tun 1993. 

Ko a matakin zaben fidda gwani na jam’iyya ko a babban zabe;  ciki har da 1993, lokacin da ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a hannun Marigayi Cif M.K.O Abiola.  

2007, lokacin da ya sha kaye a zaben shugaban kasa a hannun Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.

2011, lokacin da ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a zaben fidda gwani na shugaban kasa a hannun shugaba Goodluck Jonathan. 

2015, lokacin da ya sha kaye a zaben fidda gwani na APC a hannun Shugaba Muhammadu Buhari.  

2019, lokacin da ya sha kaye a zaben shugaban kasa a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kuma a yanzu, 2023, lokacin da ya sake, ya sha kaye a zaben shugaban kasa a hannun Tinubu.

 "Ba abin mamaki ba ne kwatsam cewa masu zabe sun ki amincewa da mai gabatar da kara na 1 a rumfunan zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023."

 Ya kara da cewa Atiku ba shi da tsayayyen tsarin siyasa, kuma ya yi asarar mafi yawan manyan magoya bayansa, duba da yadda yake tsalle daga wannan jam’iyya zuwa waccan.

 Tinubu ya kuma bayyana cewa fitowar Atiku a matsayin dan takarar PDP ya kara ruruta wutar rikicin da ke faruwa a jam’iyyar, wanda ya sa gwamnoninta biyar suka yanke shawarar yin aiki da shi tare da tabbatar da cewa ya sha kaye.

 Tinubu ya bayyana haka ne, a martanin da ya mayar kan karar da Atiku da PDP suka shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC), inda suke neman Alkali ya bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ko kuma kotu ta ba da umarnin a sake zaben.

 Tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin Cif Wole Olanipekun (SAN) ne suka shigar da martanin Tinubu a daren Laraba, 12 ga watan Afrilu.

 Ya caccaki cancantar karar, inda ya bayyana shi a matsayin ba kawai banza ba, illa dai cin zarafin tsarin shari’a ne, tun da farko PDP ta shigar da kara a kotun koli, ta hannun wasu gwamnoninta, inda ta bukaci a soke zaben.

 Ya kara da cewa PDP da Atiku ba za su iya ci gaba da shari’o’i biyu kan batu guda a kotuna daban-daban a lokaci guda ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN