Abun mamaki: An sanya wani Zomo cikin jami'an Yan sanda har da tallafin albashi a wata jihar Amurka


Wani Zomo da ake Kira da suna Percy a hukumance, shine sabon ma'aikacin Sashen 'Yan Sanda na Birnin Yuba a jihar California na kasar Amurka. Shafin isyaku.com ya samo.

 A cewar hukumar ‘yan sanda, Percy na shirin yin aiki a matsayin ‘ma’aikacin lafiya bayan an same shi ya bata kuma shi kadai a kan titi a watan Oktoban 2022.

 A cewar rahotanni, wata jami'ar Yar sanda mai suna Ashley Carson, tana sintiri lokacin da ta gano Zomon a kan titin Percy kuma ta dauke shi don ta kare shi.

Domin tabbatar da lafiyar Zomon, Jami’in Carson ya dauke shi, ya fahimci yadda yake da hankali da abokantaka’, rundunar ta bayyana a cikin wata sanarwa.

 ‘An kai Zomon wurin kula da dabbobi amma danginsa ba su yi da’awa da zuwansa cikin su ba.

 Lokacin da aka sanya Percy daga baya don karÉ“ar tallafi, nan dama ya samu inda aka saka sunan Zomon a cikin jaddawali.

 Kwanaki kafin bukukuwan Ista, ranar Lahadi, sun ba da sanarwar cewq Zomon zai ci gaba da kasancewa jami'in lafiya, wanda zai dinga tallafa wa jami'an Yan sanda.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN