Rahotanni na cewa wasu masu ruwa da tsaki na manyan jam'iyyun siyasa a jihar Kebbi sun yi wa Masarautar Zuru dirar mikiya a matakin karshe gabanin zaben Gwamna.
Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo cewa tun mako daya kafin zaben Gwamna wasu manyan Yan siyasa daga manyan jam'iyyun siyasa a jihar Kebbi suka dinga safa da marwa a Masarautar Zuru.
Masarautar Zuru ta yi fama da abin da masana ke cewa watsi da kammala cikar burin manufofin ci gaban Masarauutar daga Yan siyasa a jihar Kebbi.
Sai dai wasu na kallon cewa tare da marasa kishin Masarautar Zuru wasu Yan siyasa suka yi watsi da manufar kammala ayyukan ci gaba da na more rayuwa a Masarautar.
Gwamnatin jihar Kebbi ta kasa hada Masarautar Zuru da sadarwa na Talabijin ko rediyo, yanayi da ya mayar da al'ummar Masarautar Zuru saniyar ware wajen sanin lamurran da ke faruwa a kullum a jihar Kebbi.
Ana zargin Gwamnatin jihar Kebbi ta kashe fiye da Naira miliyan dari shidda da hamsin wajen inganta harkar watsa labarai na jihar da suka hada da daukaka matsayin watsa labarai na gidan Talabijin da rediyon jihar.
Lamari da aka ce an kammala gidan rediyo na Zuru. Sai dai har yau wannan rediyo baya aiki bayan tsawa ta fada wa karfen watsa labarai na gidan rediyon a cewa wata majiya. Har yau Gwamnatin jihar Kebbi bata gyara lamarin ba shekara takwas a karagar mulkin jihar.
Yayin da Yan siyasa suka fuskanci Masarautar Zuru gabanin zaben Gwamna, har gobe Masarautar na fama da rashin kammala hanyar Koko zuwa dabai, tabbataccen rashin tsaro, da asarar matsayin kasuwanci sakamakon wata manufa da akidar wasu Yan siyasa.
Wata majiya ta ce, bisa yadda lamurra suka kasance, tabbas Masarautar Zuru za ta kasance filin gumurzun fafatawa a sakamakon zaben Gwamna duba da yanayi da yadda yan Masarautar Zuru suka sami kansu
Sai dai a cewar wata majiya, Dan Masarautar Zuru wanda bai san ciwon kansa bane kawai zai sake tafka kuskure a ranar zaben Gwamnan jihar Kebbi.
BY ISYAKU.COM