Rundunar ƴan sandan Najeriya (NPF), tayi kakkausan gargaɗi kan maso son tada hatsaniya a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokoki na Asabar. Legit ya wallafa.
A yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnonin, ana zaman ɗar-ɗar a tsakanin jam'iyyu da magoya bayan su kan yiwuwar ɓarkewar rikici a ranar zaɓen.
Mataimakin sufeto janar na Æ´an sanda mai kula da yankin Kudu maso Gabas, John Amadi, yayi kira ga mutanen yankin da kada su yarda a sanya musu wata fargaba a rai. Rahoton The Cable
“Ƴan sanda na nan domin bayar da kariya." A cewar sa
“Duk wanda yake son sanya kan shi cikin matsala ko ya shiga cikin daba to ya kuka da kan shi. Duk wanda yayi Æ™oÆ™acin satar akwati ko tayar da hatsaniya wajen zaÉ“e zai fuskanci fushin hukuma."
"Duk wanda yake son tayar da hatsaniya to ya shirya mutuwa sannan duk wanda yake son mutuwa to ya zo ya tayar da hatsaniya. Idan kana son rayuwar ka, ka kaɗa ƙuri'a ka koma gida kawai ka jira sakamako."
Mataimakin sufeto janar din yayi kira ga mutanen jihar da su yi watsi da kowace irin barazanar hana gudanar da zaɓen, inda ya ƙara da cewa za a ba jami'an hukumar INEC cikakkiyar kariya.
Rahoton PM News
Ya bayar da tabbacin rundunar na shiryawa tsaf domin zama tsaka tsaki a lokacin zaɓen, inda yake cewa rundunar ƴan sandan bata da wata jam'iyya.
BY ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka