Tonon siriri: Gwamnatin jihar Kebbi karkashin mulkin Dan Bagudu bata san yawan mutane da Yan bindiga suka kashe ba a Masarautar Zuru daga 2019 zuwa 2023


Bisa ga dukkan alamu, Gwamnatin jihar Kebbi karkashin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu bata da cikakken alkalumman yawan wadanda Yan bindiga suka kashe a Masarautar Zuru. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Biyo bayan wasiku har guda uku na neman bayani kan adadin mutane da Yan bindiga suka kashe a Masarautar Zuru da Malam Isyaku Garba Zuru ya rubuta wa Gwamnatin jihar Kebbi.

Wasikar ta kuma bukaci wasu bayanai da suka hada da adadin yawan shanu da Yan bindiga suka sace da gidaje da suka kona da kuma wasu. 

Gwamnati ta kasa bada wannan bayani da Malam Isyaku ya nema ta dokar yancin samun bayanai Freedom of Information Act 2011 seshe na 1 (1-3) na Najeriya.

Tun ranar 9 ga watan Janairu Isyaku ya rubuta takardar neman bayanin, ya sake tunatarwa na farko ranar 6 ga watan Fabrairu daga karshe ya rubuta takardar tunatarwa ta karshe ranar 6 ga watan Maris. 

Malam Isyaku ya bi ka' idar doka kuma ya aika kofi na takardun ga ma'aikatu da ƙungiyoyin da suka dace.

Gwamnatin jihar Kebbi ta ki cewa uffan kan lamarin da ya haifar da zargin cewa Gwamnatin jihar Kebbi bata da alkalumman irin ta'asar da Yan bindiga suke aikatawa a Masarautar Zuru. 

Malam Isyaku ya ci gaba da kalubalantar Gwamnatin jihar Kebbi cewa idan har tana da wadannan alkalumma, ta fada ko ta bayar da su idan har bata da niyyar ba shi bayanan bisa akidarta na nuna masa budaddiyar kiyayya ta ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi kawai domin akidarsa ta son a kwatanta adalci.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN