Zaben Gwamna: Sanata Aishatu Binani Ta Magantu Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Adamawa


Sanata Aishatu Ahmed Binani,  Yar takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC a jihar Adamawa, ta nuna goyon bayan ayyana zaben jihar da 'bai kammalu ba.

Idan baku manta ba, baturen zaben INEC, Farfesa Muhammadu Mele, na jami'ar Maiduguri, ya ayyana zaɓen gwamnan Adamawa da bai kammalu ba watau 'Inconclusive' sabida tazarar dake tsakani.

A rahoton Premium Times, Gwamna mai ci na PDP, Ahmadu Fintiri, ya samu kuri'u 421,524 yayin da babbar mai kalubalantarsa ta AP,C, Aishatu Binani, ta samu kuri'u 390,275.

A wata hira kai tsaye a gidan Talabijin ɗin Channels cikin shirin Politics Today, Sanata Binani ta yi maraba da matakin INEC na cewa zaben bai kammalu ba.

Binani ta yi zargin cewa an samu rikici da take doka a kananan hukumomi 16 cikin 21 dake faɗin jihar Adamawa.

Ta ce:

"Matsayar dana ɗauka ita ce kwamishinan INEC na jiha ya yi daidai da ya ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba kuma dalilaina a fili su ke."

"Duk wanda ya bibiyi zaben gwamnan da aka gudanar a Adamawa ya san cike yake da tashin tashina, magudi da aringizon kuri'u da sauran abubuwan take doka."

A cewarta, tsallake na'urorin BVAS suka yi, shiyasa suka samu damar aringizon kuri'u da kuma yi wa malaman zaɓe barazana a wurare da dama.

"Alal misali, idan BVAS ta tantance mutane 10, zaka samu mutane sama da 30 sun jefa kuri'u. Wannan wani bangare ne na abinda aka aikata."

A mahangar Aishatu Binani, hanya ɗaya da REC ɗin Adamawa zai wanke kansa shi ne ta ayyana zaben a matsayin 'Inconclisive' kuma hakan ya yi.

Bayan kwanaki da gama zaɓe, baturean zaben INEC na jihar Abiya ya sanar da wanda ya samu nasarar zama sabon gwamna a jigar dake kudu maso gabas

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN