Madalla: Bayan Umarnin CBN, Bankuna Sun Aika Wa Yan Najeriya Sakon Yadda Zasu Samu Naira


A yunkurin bin umarnin babban bankin Najeriya (CBN), bankunan kasuwanci sun sanar da cewa rassansu zasu fito aiki domin mutane su aje ko cire kuɗi a ranakun karshen mako. Legit ya wallafa.

The Cable ta rahoto cewa tun da safiyar ranar Jumu'a, CBN ya sanar da cewa ya kwashe kuɗaɗen da ake hannunsa ya tura wa bankuna a faɗin kasar n

Domin sauƙaƙa wa al'umma su samu takadun kuɗi a hannunsu, CBN ya umarci bankuna da su saurari kwastomominsu a ranakun Asabar da Lahadi.

Awanni bayan wannan umarni, bankuna suka fara aika sakonnin Email, suna faɗa wa kwastomominsu su je rassan bankuna a lokacin da aka ware ranar Asabar da Lahadi domin cire kuɗi.

A sakonnin da bankunan GT da Union suka aika wa mutane a Legas, sun ce mutane da na ikon zuwa kowane reshen banki a faɗin kasa don cire kuɗi daga 9:00 na safe zuwa 4:00 na yanma.

"Dukkan rassan bankunanmu zasu buɗe ranar Asabar da Lahadi, 25 da 26 ga watan Maris, 2023 daga karfe 9:00 na safe zuwa 4:00 na yamma domin ajiya da cire kuɗi," inji Union Bank.

A wani ɓangaren kuma Standard Chartered Bank ya ce kwastomominsa zasu samu damar biyan buƙatunsu daga ƙarfe 10 na safe zuwa 3 na yamma.

"Domin sauƙaka kuncin karancin takardun naira, Muna sanar muku cewa zamu buɗe rassanmu a ranakun ƙarshen mako domin cire kuɗi daga asusu ko kawo ajiya."

"Zamu yi aiki ranar Asabar da Lahadi 25 da 26 ga watan Maris, 2023 daga karfe 10:00 na safe zuwa karfe 3:00 na rana," inji Email din da suka tura wa mutane.

2 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN