Kotun sauraren kararrakin zabe da ke birnin Kebbi, a ranar Juma’a, ta ce ta samu kararraki takwas kan zaben ‘yan majalisar dokokin jihar da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sakataren Kotun, Abdul-Rahman Muhammad, ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Birnin Kebbi. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
Ya fayyace cewa shida daga cikin korafe-korafen sun shafi zaben ‘yan majalisar wakilai ne yayin da biyu ke kan zaben majalisar dattawa.
Abdul-Rahman ya bayyana cewa Sanata Bala Ibn Na’Allah dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltar mazabar Kebbi ta kudu ya shigar da daya daga cikin kararrakin mai lamba EPT/KB/SEN/ 01/2023.
Ya kasance yana kalubalantar sakamakon zaben Garba Musa na jam'iyyar PDP.
Abdul-Rahman ya kara da cewa dan takarar kujerar Sanatan Kebbi ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abubakar Atiku-Bagudu shi ma ya shigar da kara mai lamba EPT/BK/SEN/02/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben Muhammad Adamu-Aliero na PDP.
Sakataren ya kuma zayyana karar da dan takarar jam’iyyar APC, Farfesa Muktar Umar-Bunza ya shigar mai lamba EPT/KB/HR/04/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben mazabar Birnin Kebbi/ Kalgo/Bunza na tarayya.
“Muhammad Bala-Usman na PDP mai lamba EPT) KB/HR/02/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben mazabar Yauri/Shanga/Ngaski.
"Muhammad Umar-Jega mai lamba EPT/KB/HR/03/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben mazabar Gwandu/Jega/Aliero," in ji shi.
Sauran, in ji shi, sun hada da Bello Kabiru mai lamba EPT/KB/HR/ 01/2023 yana kalubalantar sakamakon zaben mazabar Suru/Bagudo.
A cewarsa, ‘yan takarar da suka koka suna da kwanaki 21 daga ranar da aka bayyana zaben su shigar da kara a gaban kotun.
Ya ba da tabbacin cewa kotun za ta sanya ranar da za ta fara sauraren karar bayan kammala ka'idodin shigar da kara kan shari’ar daga bangarorin biyu.
BY ISYAKU.COM