Zaben gwamna: Dakyar, gwamnan APC a Zamfara ya lashe kananan hukumomi 2, PDP na da 6


Sakamakon ya nuna cewa, jam'iyyar PDP ne ke kan gaba duba da kananan hukumomi uku da aka gabatar a gaban baturen zabe, rahoton Leadership.

Ya zuwa yanzu, PDP ce ke da mafi yawan kuri'u daga sakamakon zaben da ya shigo hannun majiya. Legit ya wallafa.

PDP ta zargi APC da daukar dumi a Zamfara
A bangare guda, wani rahoton jaridar SaharaReporters na cewa, jam'iyyar PDP ta zargi ta APC da kokarin yiwa jami'an zabe barazana a wasu kananan hukumomin jihar.

A cewar PDP, dukkan sakamakon zaben da aka daura a kafar yanar gizo sun nuna PDP ce ya yiwa APC cin kaca.

Wannan zargi na PDP dai na fitowa ne daga wata nsarwar da aka a Gusau a ofishin hadimin dan takarar gwamnan jam'iyyar.

Ya bayyana cewa, alamu sun nuna gwamnatin jihar mai ci bata ji dadin yadda sakamakon zaben ke fitowa da nasarar PDP ba.

Za a ci gaba da tattara sakamakon zabe
Bayan dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Zamfara a daren jiya Lahadi 19 ga watan Maris, a yau ne za a ci gaba da kawo sakamakon daga kananan hukumomin jihar.

A jiya, an kawo sakamakon kananan hukumomi uku; Zurmi, Anka da Bukuyum, inda yau ake tsammanin kawo sauran 11 da suka rage cikin 14 na jihar.

Sauran kananan hukumomin da suka rage sune; Gusau, Tsafe, Bungudu, Maru, Bakura, Talata Mafara, Maradun, Gumi, Kaura-Namoda, Birnin Magaji da Shinkafi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN