Jihar Taraba - An samu rikici da tashin hankali a birnin Jalingo na jihar Taraba yayin da ake ta jin karan harbe-harbe a kusa ofishin INEC da hukuma hedkwatar 'yan sanda, Daily Trust ta ruwaito.
Ba a dai tabbatar da dalilin wadannan harbe-harbe ba, amma majiya ta bayyana zargin cewa, an samu sabani ne tsakanin jami'an tsaro da ke gadin ofishin na INEC. Legit ya wallafa.
An gaggauta garkame shaguna da harkokin kasuwanci, kana an ga tituna shuru yayin da iyaye ke kokari da gaggauta dauka 'ya'yansu daga makaranta.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Usman Abdullahi bai amsa waya ba, kana bai dawo da sakon tes da majiya ta tura masa ba don jin halin da ake ciki.
BY ISYAKU.COM