Abin da ya sa INEC ta ce zaben Gwamnan jihar Kebbi bai kammala ba


Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kebbi INEC ta ce ba a kammala zaben Gwamna da aka yi ba na ranar Asabar. 

Jami'in tattara sakamakon zaben Farsefa Ysusuf Sa'idu na Jami'ar Usman Dan Fodio Sokoto, ya ce an sami kuri'u fiye da yawan kuri'u da aka yi rijista kafin zaben. Equity FM Birnin kebbi ya labarta.

Ya ce dan takarar jam'iyar APC Nasir Idris ya sami kuri'u 388,258 yayin da dan takarar PDP Aminu Bande ya sami kuri'u 342,980. Dan takarar jam'iyar PRP Udu Idris ya sami kuri'u 3103.

Ya ce an soke zabuka a wasu mazabu a kananan hukumomi 20 cikin 21 a fadin jihar Kebbi.

Ya ce hakan na kunshe ne a sashe na 51 (2-3) na dokar zabe da ya ce "Idan yawan kuri'u da aka kada sun zarce yawan kuri'u da aka yi rijista a rufnar zabe. Za a soke sakamakon zabe har sai an gudanar da sabon zabe kafin a fadi sakamako".

Farfesa ya ce dokar zabe ta bayar da damar a sake gudanar da zabe a wuraten da aka sami aringizon yawan adadin masu kada kuri'a kafin a fadi sakamakon zabe. 

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Allah yazabamuna abinda yfi zama Alkhari

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN