Zaben 2023: INEC ta sanar da lokacin da Tinubu zai karbi Satifiket din cin zabe


An ayyana Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugaban kasa na 2023, a matsayin wanda ya lashe zabe. Legit ya ruwaito.

Bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye da ya kai 8,794726, an bayyana tsohon gwamnan na jihar Lagas a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023.

Bayan ayyana shi, shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da cewar zababben shugaban kasar zai karbi satifiket din cin zabe da misalin karfe 3:00 na ranar Laraba, 1 ga watan Maris.

Yakubu ya yi sanarwar ne bayan ayyana dan takarar na APC a matsayin zakaran gwajin dafin zaben a safiyar ranar Laraba, kamar yadda jaridar Legi.ng ta sanya idanu.

Jaridar Aminiya ta nakalto Mahmood yana cewa:

“A yau da misalin karfe 3:00 na rana hukumar zabe za ta ba wanda ya ci zabe takardar shaidar cin zabe.
“Daga baya hukumar zabe za ta sanar da lokacin da wadanda suka lashe zaben yan Majalisar Wakilai da Sanatoci za su samu satifiket din shaidar cin zabensu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN