Matashinnan Yusuf kowa naka da ya yi tattaki daga Birnin kebbi zuwa garin Aliero da kafa ya isa lafiya kusan La'asar. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Yusuf ya yo tattaki ne tun bayan Sallar Asuba da kafa bisa alkawari da ya dauka cewa idan Allah ya sa Sanata Adamu Aliero ya ci zaben Sanata 2023 zai yi tattaki da kafa har zuwa garin Aliero daga Birnin kebbi don nuna gidiya ga Allah.
Rahotanni na cewa Yusuf ya gamu da kalubale daga wasu matasa da suka tare shi a kan hanyarsa ta zuwa garin Aliero musamman tsakanin garin Basaura zuwa garin Jega.
Rahoton ya kara da cewa Yusuf ya jajirce kuma ya isa garin Jega lafiya kalau.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa Sanata Adamu Aliero baya gida lokacin da Yusuf ya isa garin Aliero har gidan Sanatan.
BY ISYAKU.COM